Darajar takardar kudin Rubel ta karu

Darajar takardar kudin Rubel ta karu
Darajar takardar kudin Ruble na kasar Rasha ta kai matsayi mafi girma da ba ta taba kai wa ba a cikin shekaru bakwai a kan kudin Yuro.

Kudin na Ruble wanda tsadar man fetur da iskar gas ta sa ya yi tashin gobron zabi a kasuwannin hada-hada na kudi, ya haura da sama da kishi 20 cikin dari a gaban kudin Yuro fiye da lokacin da aka soma yin yakin. A halin a ake ciki kamfanoni da yawa na Turan ya zame musu dole kaunar naki, wajen bin umarnin Putin na yin cinikayyar a Rashar da kudin Rubel. Kudin Rashan shi ne kudin duniya wanda ya fi samun ci gaba fiye da kowanne tun farkon shekara.

 


News Source:   DW (dw.com)