Ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ce ta soma fitar da sanarwar, inda a ciki ta fadi mutuwar wani dan kasar Britaniya da kuma wata da ba a gani ba tun bayan wani gumurzu da dakarun Rasha, suna daga cikin wadanda suka shiga kasar don taya Ukraine fada da Rasha.
Kafofin yada labaran Birtaniya kuwa, sun ce, akwai yiyuwar ma'aurata ne da suka shiga yakin amma ba a tabbatar da hakan ba. Tuni Ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya soma tuntubar danginsu a yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken gano wacce ba a gani ba.