Maharin ya kashe mutane 10 wasu uku sun jikkata sakamakon harin da aka kai a kasuwar sada zumunta ta Tops Friendly, hukumomi sun danganta harin da kabilanci bayan da maharin ya nuna bidiyon harin kai tsaye a shafukan sad azumunta.
An kama dan bindigar wanda ke dauke da bindiga irin na sanye da kayan yaki, an kama shi ne bayan harbin da ya yi. Jami'ai sun ce ya tuka mota zuwa Buffalo daga gidansa da ke wata karamar hukumar New York "sa'o'i kadan” don kaddamar da harin, wanda ya watsa ta yanar gizo. Mutane 11 daga cikin wadanda abin ya shafa bakar fata ne, biyu kuma farare ne. Stephen Belongia, shi jami'n hukumar FBI ne a binrin New York. "Muna binciken wannan lamarin a matsayin laifukan kiyayya da kuma batun tsattsauran ra'ayi mai nasaba da kabilanci. Hukumar FBI tana da duk abubuwan da suka dace, don binciken wannan batu. Ba za mu tsaya ba har sai an binciki kowa da komai don gano yadda tushen harin."
Daga baya an bayyana wanda ake zargin da Payton Gendron, dan garin Conklin da ke binrin New York mai tazarar mil 200 (kilomita 320) kudu maso gabashin Buffalo, kamar yadda jami'an tsaro biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press. Ba a ba wa jami'an damar yin magana a bainar jama'a kan lamarin ba, kuma sun yi hakan ne bisa sharadin sakaya sunansu.
A yanzu dai an gurfanar da Gendron a gaban kuliya bisa tuhumarsa da laifin kisan kai, wanda ke da hukuncin daurin rai da rai ba tare da sakin layi ba. Kuma ana tsare da shi ba tare da beli ba.