Lamarin da ya faru lokacin ribibin shiga jirgi da sanyin safiyar yau, bayanai sun ce ya kuma jikkata wasu mutum 13.
Shaidu sun ce abun ya yi matukar firgita jama'a ganin yadda ya faru a tashar jirgi na karkashin kasa, kuma hayaki ya tirnike wurin a lokacin.
Hukumomin yankin na Brooklyn, sun ce ba su gano wani abu mai fashewa ba a inda lamarin ya faru, kuma ana ci gaba da bincike.
Sai dai wasu jami'ai sun ce an ga wani mutum sanye da kayan kamfanin gine-gine, dauke da wata tukunyar gas a harabar.