'Dan Afghaninstan ya raunata mutane kusan 30 da mota a Jamus

Rundunar 'yan sandan Jamus ta ce kimanin mutane 28 ne suka samu raunuka a birnin Munich, bayan da wani 'dan kasar Afghanistan ya kutsa da mota cikin wasu 'yan kungiyoyin da ke jerin gwanon zanga-zangar lumana da safiyar Alhamis din nan.

Karin bayani:Wani dan Afghanistan ya kashe mutane biyu a kudancin Jamus

Sanarwar da rundunar 'yan sandan ta wallafa a shafinta na X ta bayyana maharin mai shekaru 24 da haihuwa a matsayin 'dan gudun hijira da ke samun mafaka a kasar, kuma tuni jami'anta suka damke shi, suka fara bincike a kai, don gano muradin da maharin ke son cimma wa.

Karin bayani:'Yan Afghanistan na fuskantar tuhumar kan ta'addanci a Jamus

Gwamnan jihar Bavaria Markus Söder ya bayyana lamarin a matsayin hari kai tsaye da aka shirya kai wa jama'a, inda shi kuma magajin birnin Munich Dieter Reiter ya nuna jimaminsa da yadda harin ya ritsa da kananan yara.

A ranar Alhamis aka fara shari'ar 'dan kasar Afghanistan mai alaka da kungiyar ta'addanci ta IS, bisa zargin aikata laifin kisan kai, bayan harin wuka da ya kai wa mutane a birnin Mannheim na nan Jamus, lokacin taron siyasa a cikin watan Mayun 2024.

Shari'ar na zuwa ne a daidai lokacin da babban zaben kasar na ranar 23 ga wannan wata na Fabarairu ke karatowa, wanda ke cike da muhawara kan batun yin garanbawul ga dokar bai wa bakin haure damar shigowa kasar, sakamakon yawaitar aikata muggan laifuka da ake fuskanta a Jamus daga bakin haure da 'yan gudun hijira masu neman mafaka.

Maharin mai suna Sulaiman A, ya cakawa mutane 6 wuka, cikinsu har da 'dan sanda guda da tuni ya riga mu gidan gaskiya sanadiyyar raununkan da ya samu daga harin wukar.


News Source:   DW (dw.com)