Tawagar ta yi kira ga kasashen Lebanon da kuma Isra'ila da su mutunta kudirin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 a aikace a matsayin mafita daya tilo da za a mayar da zaman lafiya a yankin.
Kudirin na kwamitin sulhu da ya kawo karshen yakin shekarar 2006 da aka gwabza a tsakanin Isra'ila da Hizbollah ya amince da cewar sojojin Lebanon da dakarun wanzar da zaman lafiya ne kadai aka amince su kasance a kudancin Lebanon.
To sai dai tun a farkon wannan makon sojojin Isra'ila suke kokarin kutsa kai ya zuwa yankuna da dama a kudancikn kasar ta Lebanon.