Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da jagoran 'yan adawa a Jamus mai ra'ayin mazan jiya Friedrich Merz, ya nufi Kiev babban bibnrin kasar Ukraine bayan da Shugaban gwamnatin Jamus Chancellor Olaf Scholz ya soke ziyararsa.
Shugabannin Ukraine sun koka kan jan kafar da Jamus ke yi na tsawon makonni wajen raba gari da gwamnatin Moscow, kuma sun soki kasar kan yadda take nuna shakkun na kai agajin manyan makamai zuwa Ukraine domin yakar sojojin Rasha.
Matakin hukumomin gwamnatin kyiev na kin maraba da ziyarar shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a baya-bayan na, ya kara dagula alaka tsakanin kasashen guda biyu.