Dakarun Nijar sun mutu a harin ta'addanci

Dakarun Nijar sun mutu a harin ta'addanci
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an kashe dakarunta 8 yayin da wasu 33 suka jikkata a wani harin ta'addanci da aka kaddamar a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.

A cikin sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce, maharan sun kai hari garin Waraou da ke kudu maso gabashin kasar a kan babura, wanda a halin yanzu wasu dakarun tsaron kasar shida da su ma harin ya rutsa da su ke cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai. Sanarwar ta kuma kara da cewa maharan sun lalata motoci 5. Ma'aikatar ta ce tuni aka fara kaddamar da bincike kan harin.

Sai dai yayin musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, mahara 50 ne suka mutu. Ko a bara, wasu ma'aikatan hukumar zaben kasar sun rasa rayukansu a yankin na Waraou bayan da motarsu ta taka nakiya. 

Jamhuriyar Nijar dai ta sha fama da matsalolin tsaro da na kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai mussaman a yankunan da ke kan iyakokinta da kasashen Mali da Burkina Faso.
 


News Source:   DW (dw.com)