Dakarun Isra'ila sun ragargaza cibiyar sojoji mafi muhimmanci ta kasar Siriya. Hakan ya faru ne a yayin wasu sabbin hare-hare da Isra'ila ta kaddamar tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.
Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya ce wadannan hare-hare da kasarsa ta kaddamar kusa da iyakarta da Siriya a tuddan Golan inda Isra'ilan ta mamaye, ta yi haka ne domin inganta tsarontana cikin gida, kuma a cewarsa matakai ne na wucin gadi ba na din-din ba.
Har kawo safiyar wannan Talata dai kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ce ana ci gaba da jin karar abubuwa masu fashewa a birnin Damascus, hedikwatar mulkin kasar Siriya.