Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bayyana cutar kyandar birrai da ta bulla a baya-bayan nan a nahiyar da cewa ta zama matsalar lafiya da ke bukatar matakan gaggawa.
Tuni ma hukumar lafiya ta duniya WHO, ta kafa kwamitin kwararru na gaggawa da zai tattauna batun wannan cuta da aka gani cikin kasashen Afirkar 18.
Ya zuwa yanzu dai cikin wannan shekarar, an samu mutum dubu 15 da cutar ta kyandar birrai ta kama, inda mutane 461 suka mutu da ita.
Cutar ta fara ne daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da samfurin farko na Clade I yayin kuma da aka samu samfuri na biyu na Clade Ib daga bisani da ke da saurin yaduwa a tsakanin musamman kananan yara.
An dai bayyana cewa kwayar cutar ba ta nuna matukar alamu na karfi ba, sai dai kuma tana iya kisa.
Sama da mutum miliyan 10 ne ke bukatar samun allurar rigakafin kyandar birran a Afirka a halin yanzu a cewa hukumar lafiyar duniyar WHO.