Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta samar da karin alluran rigakafin kwalara 455,000 a Sudan domin taimaka wa kasar tunkarar sabuwar annobar amai da gudawa da ta barke. A ranar 12 ga watan Agusta ne kwalara ta sake konno kai a Sudan bayan kawo karshen bullar ta a watan Mayun da ya gabata, inda fiye da mutane 11,300 suka kamu da kwalara yayin da fiye da 300 suka mutu.
Karin bayani: Me ya sa cutar kwalara ke karuwa a duniya?
WHO ta ce a halin yanzu, sabuwar kwalarada ke haddasa annobar ta amai da gudawa ta kama mutan 658 yayin da mutane 28 suka mutu a jihohi 5 da suka hada da Kassala da Gedaref da al-Jazeera, da Khartum. Sai dai yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane da dakarun Janar Mohamed Hamdane Daglo na kawo cikas wajen kai magunguna da sauran kayan agaji ga mabukata.