Zaftarewar kasar ta afku ne daga daran jiya Larba zuwa yau Alhamis, wanda aka yi ta samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a gundumar Mossikro da Attécoubé da ke yammacin birnin Abidjan. A birnin na Abidan an saba samun zaftarewar kasar a lokacin damina musammun ma a unguwani marasa galihu. A watan Yunin shekara ta 2018 mutane 18 ne suka mutu a Abidjan bayan mamakon ruwan sama. Wasu kuma 13 suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a watan Yunin shekara ta 2020.