COP29: An ware kudin yakar matsalar sauyin yanayi

Sai dai kuma kudin da aka amince a yayin taron sauyin yanayi na duniya na bana wato COP29 da ya gudana a Azerbaijan, bai kai kusa da adadin da kasashe masu tasowa suka bukata ba. Duk da kwashe tsawon kwanaki ana gaba ana baya a taron, wakilan manyan kasashen sun ce wannan yarjejeniyar tana kan daidai, tare da fatan samar da karin kudi a nan gaba. Ko da yake dai, masu wakiltan kasashen masu karamin karfi sun fice daga zauren taron na sauyin yanayi.

Ana dai sa ran wannan kudin ya taimakawa kasashen wajen daidaita matsalar dumamar yanayita kuma diyya ga irin barnar da sauyin yanayi ya haddasa musu.

 


News Source:   DW (dw.com)