Compaore zai kare rayuwarsa a yari

Compaore zai kare rayuwarsa a yari
Wata kotun soji a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai-da-rai, kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Shugaban juyin juya hali na kasar Thomas Sankara a shkearar 1987.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Hyacinthe Kafando, jami'in da ake zargi da jagorantar rundunar da aka kai harin shekaru 37 da suka gabata, da kuma Janar Gilbert Diendere, kwamandan sojoji a lokacin kisan.

Blaise Compaore mai shekara 71 a duniya, wanda ke gudun hijira a kasar Ivory Coast bayan da aka hambarar da shi sakamakon zanga-zangar da jama'a suka yi a shekarar 2014, da kuma Kafando, wanda ke gudun hijira tun 2016, an yi musu shari'ar ne a bayan idonsu.


News Source:   DW (dw.com)