China ta yi nisa wurin kera makaman nukiliya. Ministan tsaron kasar Wei Fenghe ne ya sanar da haka a wannan Lahadi a yayin taron koli kan harkokin tsaron yankin Asiya da ke gudana a Singapore. Ministan ya ce shekaru sama da 50 suka kwashe suna kokarin kera makamin.
Tun a shekarar da ta gabata Amirka ta ce ta bankado yadda China ke bunkasa makamashin nukiliya ba tare da sanin duniya ba. To sai dai ministan tsaron Chinan ya ce burin kasarsa shi ne kokari na dakatar da amfani da makamin kare dangi a duniya ta hanyar kare martabarta.