China ta yi karin harajin kashi 15% kan Amurka

China ta ce ta dora harajin ne akan makamashin da Amurka ke shigarwa kasarta da motoci da kuma wasu kayayyaki, a wani mataki na mayar wa kura aniyarta lamarin da ke kara rura wutar yakin cinikayya a tsakanin manyan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki.

A ranar Asabar da ta gabata Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da daukar gagarumin mataki akan manyan kasashe abokan kasuwancin kasarsa da suka hada da Kanada da Mexico da kuma kayayyakin China da karin haraji na kashi goma cikin dari 

China dai babbar kasa ce da Amurka ke sayar wa makamashi inda alkaluman hukumar kwastam a Beijin suka nuna Amurka ta sayar wa China makamashin fetur da Kwal da iskar gas da kudin su ya kai dala biliyan bakwai a shekarar da ta wuce

 


News Source:   DW (dw.com)