Karfin tattalin arzkin kasar ta biyu mafi girma a duniya ya ragu fiye da yadda ake tsamani saboda dokar kule da gwamnatin ta kakaba a kasar. Ofisfin kididiga na birnin Bejin a wani rahoton da ya bayyana ya ce haɓakar masana'antu ta faɗi a cikin watan Afrilu da kashi biyu da digo tara cikin dari, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kana rashin aikin yi, ya karu da kishi shida cikin dari.