Kafar yada labaran China ta ce gwamnatin kasar ta daure wasu mutum 15 da ke da hannu a gina wani katafaren gini da ya rufta kan gomman mutane a kasar.
A watan Afrilun 2022 ne wani gini da ake amfani da shi wajen cinikayya ya rufta kan jama'a a birnin Changsha na tsakiyar kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sama da mutum 50 tare da jikkata wasu tara.
Karin bayani: Guguwar Yagi ta yi ta'adi a Vietnam da China
Daga bisani hukumomi sun bayyana cewa ba a bi ka'ida ba wajen yin ginin, abinda ya jawo cece-kuce kan cin hanci da rashawa a harkar gine-ginen kasar.
Kafar yada labaran China CCTV ta ce wasu kotuna biyu a birnin na Changsha sun yanke hukunci kan mutum 15 da ke da hannu a faruwar al'amarin.
Karin bayani: Sojojin China na gagarumin atisaye kusa da Taiwan
Wasu daga cikin mutanen da hukuncin ya shafa kamar Wu Zhiyong mazauni a inda ginin ya rufta zai shafe shekara 11 a magarkama.