Kafar yada labaran Bloomberg ya ruwaito cewa hukumomin China na duba yiwuwar sayar da kadarorin TikTok a Amurka ga Elon Musk. Kafar sada zumuntar na kan siradi ko dai a sayar da shi ga wani a cikin Amurka ko kuma a rufe shi baki daya a kasar. Tattaunawar sayar TikTok din na matakin farko ne a yanzu.
Kafar sadar zumuntar mallakar kamfanin ByteDance na da hedikwata ne a China
A baya bayan nan an yi ta tada jijjiyar wuya a Amurka kan kamfanin na China bisa fargabar saba dokar kundin adana bayanai.
Gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa China na amfani da TikTok wajen tatsar bayanai da yin leken asiri kan masu amfani da dandalin tare ma da yada farfaganda. Zarkin kuma da gwamnatin China da kamfanin ByteDance suka musanta.