China da Kanada da Mexico sun mayar wa Amurka da martanin haraji

Firaministan Kanada Justin Trudeau ya dauki matakin kakabawa kayayakin Amurka harajin kashi 25 cikin 100 na hajar Amurka da za su shiga Kanada na sama da dala biliyan 155. Firamista Trudeau ya ce Trump na kokarin ya raba kasashen da suka jima suna alaka tare, sama da kaso 75 na kayayakin da Kanada ke fitarwa na karewa ne a Amurka.

Kunshe a cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar kasuwancin China ta yi Allah wadai da matakin karin harajin, Beijing ta sha alwashin kalubalantar wannan karin a gaban kungiyar kula da harkokin kasuwanci WTO, a cewar Beijing wannan karin ya saba ka'idojin kungiyar.

ita ma a nata bangaren shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum ta bayyana cewar ta umurci ministan tattalin arzikin kasar da ya mayar da martanin da ya dace, kazalika ta kuma yi tir da zargin da Washington ta yi musu na cewar suna da alaka da masu safarar miyagun kwayoyi.

Ko baya ga wadannan kasashen kazalika Shugaba Trump ya ce zai saka wani sabon haraji ga kasashen EU duk a kokari na ciyar da kasarsa gaba.

Ana ganin dai wannan matakin karin harajin musamman ga kasashen da ke makwabtaka da Amurkan ka iya jefa su a cikin wani yanayi na tabarbarewar tattalin arziki, wanda kuma ka iya ruguza kasuwannin hada-hadar kudi a duniya.

Karin Bayani:Donald Trump zai kara haraji kan China da Mexico da Kanada


News Source:   DW (dw.com)