Chaina ta yi wa Pelosi barazana kan Taiwan

Chaina ta yi wa Pelosi barazana kan Taiwan
Kasar Chaina ta bayyana cewa za ta dauki tsauraran matakai idan shugabar majalisar wakilan Amirka Nancy Pelosi ta ziyarci Taiwan.

Wani rahoto jaridar Financial Times ne ya nunar da cewa Pelosi na shirin kai ziyara Tsibirin mai cin gashin kansa, wanda kasar Chaina ke ikirarin cewa mallakinta ne. Tun da farko dai, an shirya ziyarar a watan Afrilu amma Nancy Pelosi ta dage ta bayan ta kamu da COVID-19.

Kasar Sin ta sha alwashin mamaye yankin Taiwan da karfi idan zarafi ya kama, kuma ta yi shawagi da jiragen yaki a kusa da sararin samaniyar Taiwan tare da gudanar da atisayen soji domin nuna karfin makamanta. Fadar mulki ta Beijing ta zafafa kalaman da take yi wa Amirka, inda take neman a soke yarjejeniyar kusan miliyan 108 na dollar Amirka da aka cimma da Taiwan domin inganta tsarin tsaronta.

 


News Source:   DW (dw.com)