Chaina ta kaddamar da sabbin atisayen soji a kusa da Taiwan

Rahotanni sun yi nuni da cewa, ana gudanar da atisayen ne a yankunan arewaci da kudanci da kuma gabashin Tsibirin Taiwan. Hakan dai na zuwa ne, mako guda bayan da Shugaban kasar Taiwan, Lai Ching-te ya sha alwashin hana duk wani yunkuri na mamaye tsibirin a wani jawabi da ya gabatar.

Ma'aikatar tsaron Chaina ta ce atisayen ya zama wajibi ne domin kare martaba da ma hadin kan 'yan kasa. Sai dai a martaninta, Taiwan ta yi Allah wadai da atisayen tare da bayyana shi a matsayin tsokana. Kawo yanzu ba a bayyana ranar kamalla atisayen sojin ba.

 


News Source:   DW (dw.com)