Chadi ta musanta kashe fararen hula yayin yaki da 'yan ta'adda

Gwamnatin Chadi ta musanta rahoton da ke cewa sojojinta sun kai hari kan fararen hula lokacin da suke gumurzu da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi, bayan da rahotanni ke nuni da yadda dakarunta suka halaka wasu masunta a kusa da iyakarta da Najeriya.

Karin bayani:Chadi ta bukaci taimako kan yaki da ta'addanci

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin ta Chadi Abderaman Koulamallah ya fitar, ta ce sojojinta sun kai farmaki kai tsaye kan tungar 'yan ta'addan bayan gano maboyarsu, kuma suna sajewa ne da masunta a ko da yaushe, musamman ma idan suka kai harin sari ka noke ga sojojin kasar.

Karin bayani:Chad:Barazanar ambaliya saboda cikar kogunan Logone da Chari

A ranar Larabar da ta gabata ne wani harin ta'addanci ya halaka sojojin Chadi 40, lamarin da harzuka mahukuntan kasar, har ma shugaban kasar Mahamat Idriss Deby ya sha alwashin jagorantar sojojin da kansa don daukar fansa, lokacin da ya kai ziyara sansanin sojin da aka kai wa harin.


News Source:   DW (dw.com)