Kasar Chadi ta bukaci gamaiyar kasa da kasa su kara azama ta fuskar taimako na yaki da ta'addanci a yankin Sahel, bayan harin mayakan Jihadi da ya kashe sojojin Chadi 40 a wani harin ba zata.
Kungiyar Jihadin a ranar Lahadin da ta gabata, ta kai hari kan wata bataliyar soji a yankin tafkin Chadi, yankin da ya yi kaurin suna wajen kungiyoyin yan bindiga a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Abderaman Koulamallah ya fitar.
Majiyoyin sojin sun ce wasu mutanen kimanin 20 sun sami raunuka a harin.