Chadi ta ayyana dokar ta baci

Chadi ta ayyana dokar ta baci
Kasar Chadi ta ayyana dokar ta baci saboda hauhawar farashin kayan abinci sakamakon yakin Ukraine.

Shugaban gwamnatin mulkin soji Mahamat Idriss Deby, ya yi gargadin karuwar hatsari ga al'ummar kasar idan ba a kai agajin jin kai ba Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan biyar da rabi a yankin Sahel za su iya dogaro da tallafin jin kai a bana. Sakamakon harin da Rasha ta kai wa Ukraine farashin gero ya yi tashin gwauron zabi a bisa kasuwanni. Kusan kashi 30 cikin 100 na alkama da ake samarwa a duniya na zuwa ne daga kasashen biyu wato Rasha da Ukraine.

 


News Source:   DW (dw.com)