Wakilai dubu da 400 ne da suka hada da na gwamnati da banagrorin siyasa na kungiyoyin fararen hula gami da na 'yan tawaye ne ke taron na kasa a N'Djamena babban birnin kasar Ta Chadi.
Taron da aka tsara yi cikin makonni uku domin tsayar da lokacin da za a yi zabe a kasar, bayanai na cewa an fuskanci jinkirin fara shi sannan wasu ma sun bijire masa.
Hankali dai ya fi karfi a kan bangaren 'yan tawaye da suka jima suna jayayya da gwamnati da kuma batun da ya shafi kundin tsarin mulkin Chadin.
Shugaban gwamnatin sojan kasar, Mahamat Idriss Deby ne dai ya shirya taron inda ake sa ran ya yi jawabi da misalin karfe 10 na safiyar ta Asabar agogon kasar.
Faransa da kungiyar Tarayyar Afirka wato AU ne dai suka bukaci shugaban na Chadi da ya yi kokarin maida mulki ga zababbiyar gwamnati a Chadin.