Chadi da Nijar za su zaburar da G5 Sahel

Chadi da Nijar za su zaburar da G5 Sahel
A wata ganawa a birnin N'Djamena na kasar Chadi, shugabannin kasashen Nijar da Chadin sun ce za su sake karfafa rundunar G5 Sahel wadda Mali ta fice daga ciki.

Shugabannin kasashen Chadi da Nijar, sun yi alkawarin sake karfafa rundunar nan ta G5 Sahel domin ci gaba da yaki da ayyukan tarzoma a yankin, bayan ficewar da kasar Mali ta yi a baya-bayan nan.

Sai dai Shugaba Bazoum Mohamed na Nijar a tattaunawarsa da Mahamat Idriss Deby a N'Djamena babban birnin kasar Chadi a ranar Laraba, ya lullube batun dawowar sojojin Faransa a yankin.

Shugaba Bazoum ya ce akwai wata ganawar da ke tafe a tsakanin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mauritania da Nijar da nufin sake zaburar da rundunar ta G5 Sahel.

Kuma matakin ficewar Mali daga cikinsu, wani abu ne da ya riga ya zama labari, a cewar Shugaba Bazoum.

Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai gwamnatin soja a Mali ta sanar da tsame kanta daga rundunar ta hadaka da aka kafa a shekara ta 2014 don yakar mayaka masu ikirarin jihadi da ke addabar kasashen da ma wasu makwabta.


News Source:   DW (dw.com)