Duk da cewar 'yan majalisar dokokin Jamus sun yi watsi da kudirin dokar da jam'iyyar CDU ta gabatar kan tsaurara matakan karbar 'yan gudun hijira, dubban mutane ne da suka hada da 'yan siyasa da 'yan kungiyoyin fararen hula ciki har da masu rajin kare hakkin dan Adam da masu goyon bayan shigar baki kasar ne suka fantsama kan tituna a manyan biranen kasar don yin gangami na nuna adawarsu da matakin CDU.
A birnin Bonn ga misali, fiye da mutum dubu goma ne suka halarci gangamin inda aka gudanar da jawabai iri-iri na nuna adawa da 'yan siyasa masu kyamar baki da kuma yin Allah wadai da jam'iyyar CDU da ta yi aiki da su a makon jiya, lamarin da ya sanya mutane barkewa da sowa da tafi a lokacin da guda daga cikin masu jawaban ta nuna cewar Bonn ba za ta taba amincewa da duk wani yunkuri na nuna kyama ko wariya ga kowa ba.
Karin bayani: Jamus: Kudirin tsaurara dokar shige da fice
DW ta samu zantawa da wasu daga cikin wadanda suka halarci wannan ganganmi inda bakinsu ya zo daya kan kare hakkin dan Adam da demokradiyya da kuma yin dukannin mai yiwuwa wajen hana 'yan siyasar da ke kyamar baki yin rawar gaban hantsi a fagen siyasar Jamus.
Karin bayani: Olaf Scholz ya caccaki manufofin Merz na bakin haure Yayin da ake ci gaba gangami makamancin wannan a sassan Jamus daban-daban, 'yan siyasa na ci gaba da yakin neman zabe na zaben 'yan majalisar da zai gudana nan da makwanni ukun da ke tafe, yakin neman zaben da batun karbar 'yan gudun hijira da nuna wariya ke ci gaba da zama baban jigon da ake tattaunawa a kansa.