Cibiyar ta CDC dai ta yi wannan kiran ne a wani mataki na tallafawa kamfanin Aspen don ci gaba da samar da alluran a nahiyar a cikin sauki da ma rahusa.
A kokarin da cibiyar ke yi na ganin kamfanin da ke samar da alluran bai kai ga durkushewa ba a sabili da rashin masu sayen rigakafin.
Mataimakin darakatan kamfanin ya ce duk masu sayen alluran daga kasashen Turai ya kamata su karkata akalarsu ga wadanda aka samar a gida.
Wannan dai shi ne kamfanin farko da ya fara samar da rigakafin corona a nahiyar Afirka, amma rashin samun masu sayen alluran rigakafin da suka samar na barazana ga durkushewar kamfanin.