Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta rushe dogon ginin nan mai hawa 24 na Grenfell Tower da ke birnin London inda aka yi mummunan gobara da ta hallaka mutane da dama.
A lokacin da gobarar da tashi hayaki ya turnuke ginin mai tsawo da ke yammacin london da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Yunin 2017 da ya sanadiyar mutuwar mutane 72
Gobarar ta bankado da irin almundahanar da kamfanonin gine-gine ke yi da raunin gwamnati wajen sa ido da kuma halin ko in kula na jami'an kananan hukumomi.
Sai dai wasu daga cikin mutanen da suka tsira daga gobarar sun ce suna so a bar ginin a haka a matsayin abin tarihi domin tunawa da wadanda suka rasu a iftila'in gobarar.