Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya fadi cewa a jiya Asabar ''dole ne nahiyar Turai ta zabura domin taka rawar gani a cikin kungiyar tsaro ta NATO tare kuma da yin aiki kafada da kafada Amurka don ceto makomar Ukraine''.
Kier Stamer ya kuma kara da cewa Burtaniya za ta yi duk mai yiwuwa don ganin Amurka da nahiyar Turai sun ci gaba da tafiya tare, sannan kuma ba za a yi sake ba abokan gaba su ci gajiyar rarrabuwar kawuna a cikin kawancen tsaro na NATO da ke neman raba hankalin membobin wannan kungiya.
Karin bayani: Jamus: Kasashen duniya na taro kan tsaro a Munich
Wadannan kalamai na firaministan Burtaniya na zuwa a daidai lokacin Tarayyar Turai ke da yakinin cewa tsaron nahiyar na cikin hadari sakamakon matsa kaimi da gwamnatin Donald Trump ke yi a game da tattauna kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.