Sojojin Burkina Faso sun ce za su gano tare da tattaunawa da 'ya'yan kungiyoyin da suka hana Burkina Faso zaman lafiya domin a dinke barakar da ke faruwa, a dawo da zaman lafiya a kasar da ke Afirka ta Yamma.
Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso ta kafa kwamitin da zai tattauna yiwuwar sulhu da mayakan jihadi da suka jima suna kai hare-hare a kasar. Laftanar Janar Paul-Henri Sandaogo Damiba, shugaban sojojin da suka kwace mulki a watan Janairu, ya fadi haka ne a yayin jawabin da ya yi wa 'yan kasar a birnin Ouagadougou a yammacin ranar Jumma'a.
A lokacin da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Roch Marc Kabore, sun ce kamarin da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi ke yi ne ya tilasta su kifar da gwamnatin ta dimukurdiyya. Sai dai watanni kusan uku da karbewar, matsalar na ci gaba da ruruwa.