Burkina Faso: Mahara sun kashe 'yan sanda 10

Burkina Faso: Mahara sun kashe 'yan sanda 10
Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan jihadi ne sun halaka 'yan sandan gwamnati 10 a arewacin kasar Burkina Faso da ke kusa da iyaka da Nijar.

Wata majiya ta ce, "A daren ranar Alhamis ne 'yan ta'adda suka kai hari a wani sansanin Jandarma a Seytenga da ke lardin Seno." Majiyar ta kara da cewa "Kimanin jandarmomi 10 sun mutu, hudu sun samu raunuka, an kuma yi barna sosai,” akwai yuwar adadiny a karu inji majiyar.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da harin, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren zubar da jini a kasar Burkina Faso. Majiyar ta kara da cewa jami'an tsaro sun fatattaki maharan a wani hari da suka kai musu, inda a yanzu haka suke farfasa wurin.

"Har yanzu ba a ga wasu dakaru da dama ba" har zuwa safiyar Juma'a, in ji majiyar ta biyu. Daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, Burkina Faso ta fada cikin rikici na kusan shekaru bakwai da mayakan jihadi suka tsallaka daga makwabciyar kasar Mali.

Wannan harin dai ya faru ne bayan wani harin a jiya Alhamis ya kashe jami'an tsaro a yammacin lardin Kossi da wani hari a mahakar zinari a arewacin kasar.

Hare-haren 'yan ta'adda a Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 2,000, a yayin da kusan mutane miliyan 2 sun tsere wa gidajensu sakamakon ayyukan ta'addanci musamman a arewacin kasar.


News Source:   DW (dw.com)