Burkina Faso: Barazanar yunwa a arewaci

Burkina Faso: Barazanar yunwa a arewaci
Kungiyar Medecin San Frontiere ta ce mazauna garin Shebba, babban birnin lardin Yagha da ke arewacin Kasar Burkina Faso, na cikin hali na tasko.

Tsawon wata guda garin ya kasance datse da sauran yankunan Burkina Faso sakamakon kawanya da masu jihadi suka yi masa. Manajan ayyukan kungiyar  ta Medecin Sans Frontiere ko Doctors Without Borders Ulrich Crepin ya ce hanyar da ta hada garin na Shebba da Dori ta tsinke ba shigi ba fici saboda masu kai hare-hare. Darakatan na Medecin Sans Frontiere ya ce akwai rishin abinci, mutane na cin ganye domin su rayu, ya yi gargadin cewar idan ba a yi wani yunkuri ba a cikin  kwanki masu zuwa yankin zai fuskanci wani mummunar bala'i na rishin abinci,na yunwa. Mutane kusan dubu 30 suke zaune a garin na Shebba da ke a arewacin Burkina Faso.

 


News Source:   DW (dw.com)