Bundestag za ta yi muhawara kan Ukraine

Bundestag za ta yi muhawara kan Ukraine
Nan gaba aka shirya majalisar dokokin Jamus Bunestag za ta tafka muhawara a game da wani daftarin kudiri na bai wa Ukraine manyan makamai na yaki.

An dai kai ga mika kudirin ga majalisar dokokin ne, bayan kwashe makwanni ana takun saka, tsakanin jam'iyyun adawa da hadakar jam'iyyun siyasa na SPD da Greens da FDP wadanda a karshe suka cimma matsaya. A yammacin jiya ne Larba shugabannin jam'iyyun siyasar suka saka hannu a kan amincewa da kudirin.

 


News Source:   DW (dw.com)