Bukatar sake gina Zirin Gaza daga Masar

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar tare da firaministan Spaniya a birnin Madrid. Wannan kira na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kwace iko da yankin, abin da ya harzuka Larabawa. Ana sa ran shugabannin kasashen Masar da Saudiyya da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar za su gana a birnin Riyadh na Saudiyya, domin tattauna batun sake tsugunar da al'ummar Gaza da kuma kwace iko da yankin da Trump ya ayyana.


News Source:   DW (dw.com)