Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su tsagaita wuta albarkacin bikin Easter da ke tafe.
A jawabin da ya yi a yau Lahadi, Fafaroma ya bukaci bangarorin da ke kai ruwa rana da su mutunta wannan lokaci su maida wukaken su kube don kawo karshen yakin baki daya.
Wannan jawabi dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin kara taimaka wa Ukraine da manyan makamai da za ta kare kanta a yayin da Rasha ke zafafa kai hari a gabashin kasar.
Ko a wannan rana ta Lahadi an kai wani hari a filin jirgin sama da ke garin Dnipro da ke gabashin kasar baya ga na jirgin kasa da aka kai a Juma'ar da ta gabata wanda ya hallaka sama da mutane 50.