Kotun kolin Brazil ta tabbatar da hukuncin da alkalai suka yanke a makon da ya gabata na toshe kafar sada zumunta na X mallakar Elon Musk bayan da kamfanin ya ki sanar da wakilinsa a bangaren shari'a. Alkalai biyar suka yanke hukuncin karkashin jagorancin Alexander de Moraes.
Musk da magoya bayansa sun yi kokarin nuna Moraes a matsayin wanda ya butulce kuma dan kama karya da ya tauye yancin fadin albarkacin baki.
Matakin na Moraes ya zo ne bayan da shafin X da aka fi sani da Twitter a da ya kasa bin umarnin kotu na baiyana sabon wakilinsa kan batutuwan da suka shafi shari'a a kasar ta kudancin Amurka kafin cikar wa'adin da aka ba su.
Dokokin Brazil dai sun tanadi cewa wajibi ne dukkan kamfanonin Internet su samar da wakili kan batutuwan da suka shafi kara ko shari'a don tabbatar da cewa idan mutum ya shigar da karar kamfanin an san wanda za a tuntuba.