Brazil ta haramta wa Bolsonaro halartar bikin rantsar da Trump

Mai shari'a Alexandre de Moraes da Bolsonaro ke gani a matsayin abokin adawarsa, ya shaida cewar, tsohon shugaban ba shi da wani hurumin wakiltar Brazil a ko'ina, bugu da kari bai ma gabatarwa kotu shaidar da ke tabbatar da cewa an gayyace shi bikin rantsuwar ba.

Rundunar 'yan sandan kasar ce ta kwace masa fasfo a cikin watan Fabarairun bara, bisa tarin zarge-zargen da ake masa na aikata laifuka, ciki har da kin barin kujerar shugabancin Brazil, duk kuwa da shan kayen zabe da ya yi a hannun Luiz Inácio Lula da Silva.

Tun farko dai Bolsonaro, ya roki kotun da ta bada umarnin mayar masa da fasfo domin yin bulagaro a gobe Juma'a 17 ga watan Janairu, sannan ya koma gida ranar 22 ga watan.


News Source:   DW (dw.com)