Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kammala ziyara a birnin Landan wadda ke zama ran gadi na 11 da yake yi tun bayan barkewar rikicin Gaza sai dai a wannan karo ma jami'in bai samu nasarar cimma wata yarjejeniya kan tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna ba. Tun da farko dai Blinken ya yi ittifakin cewa a wannan karo bangarorin za su amince da tsarin da Amurka za ta gabatar musu, sai dai amma ba zato ba tsammani aka watse baram-baram.
Karin bayani: Amurka ta bukaci kawo karshen yakin Gaza
Abin da ya hana ruwa gudu wajen cimma yarjejeniya shine batun kawar da kungiyar Hamas daga madafun ikon Gaza, dan karamin yankin na Falasdinu mai yawan jama'a da ke karkashin ikonta tun shekarar 2007.
A daura guda a yayin ganawar da jami'in diflomasiyyan ya yi da ministocin kasashen Larabawa a birnin Landan, ministan harkokin wajen Jordan Ayman Safadiya yaba wa kokarin Amurka na warware rikicin Gaza, amma sai dai ya dasa ayar tambaya kan rashin tasirin Washington a kan firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.