Blinken na ziyarar aiki a kasar kwango

Blinken na ziyarar aiki a kasar kwango
Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya isa Jamhuriyyar Dimukaradiyyar Kwango, a wata ziyarar aiki ta wuni guda da ke da nufin kawo karshen rikicin da kasar ke yi da makwabciyarta Ruwanda.

Wannan ziyar ta Blinken na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta kwango ke neman taimakon kasashen ketare a rikicinsu da Ruwanda musamman ma a kan mayakan kungiyar nan ta M23 da a baya-bayan nan lamarin ya kazanta.

Shugaba Felix Tshisekedi zai yi zama na keke da keke da mista Blinken a fadar mulki da ke Kinshasa, inda zai bukaci kyautata alakar diflomasiyar kasarsa da Amirka.

Gabannin wannan ziyara, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human right Watch  ta bukaci sakataren Amirkan da ya yi Allah wadai da hare-haren kungiyar M23 da kuma bukatar matsin lamaba ga Ruwanda a kan batun cin zarafin al'umma

 


News Source:   DW (dw.com)