Mutane akalla 30 da Birtaniya ta zarga da shiga kasar ba bisa kaida ba, za a mayar da su Ruwanda a yau, tun farko an dage batun mayar da su Ruwanda a sakamakon karar da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil'Adama suka shigar na kalubalantar matakin mahukuntan Britaniyan amma bayan rashin nasara a gaban kotun daukaka karar aka ci gaba da aiwatar da shirin.Britaniya ta cimma yarjejeniyar dala miliyan 151 da Ruwanda kan karbar mutanen
Nan gaba a yau zuwa da yamma aka shirya jirgin farko na wadanda Birtaniya ta hanawa mafaka zai sauka a birnin Kigali na kasar Ruwanda.