Birtaniya za ta kori baki zuwa Ruwanda

Birtaniya za ta kori baki zuwa Ruwanda
Birtaniya na fuskantar mumunar adawa a kan shirinta mai cike da cece-kuce, wanda gwamnatin ta gabatar ga majalisar dokokin kasar na tura masu neman mafaka da suka isa kasar ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Ruwanda,

Shugaban gwamnatin na Birtaniya Boris Johnson da ke yin jawabi a garin Kent da ke kudu maso gabashin kasar, ya ce duk wadanda suka shiga Birtaniya ba bisa ka'ida ba tun daga farkon watan Janairu dama wadanda ke zaune a kasar da dadewa za a tisa keyarsu zuwa Ruwanda. MDD da kungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty international sun yi Allah wadai da matakin da suka kira koma bayan a kan sha'anin kare hakkin dan Adam.

 


News Source:   DW (dw.com)