Birtaniya: Oliver Dowden ya yi murabus

Birtaniya: Oliver Dowden ya yi murabus
Shugaban jam'iyyar Conservative ta Birtaniya Oliver Dowden ya sanar da ya da kwallo don ya rabu da kuda, bayan shan kayen da jam'iyyarsa ta yi a zabukan 'yan majalisar dokoki biyu da aka gudanar ranar Alhamis.

Cikin wata wasika zuwa ga Firayiminista Boris Johnson, Dowden ya ce wannan wulakanci "ya kasance na baya bayan nan a jerin munanan sakamako ga jam'iyyarsa ta samu a zabuka, wanda ya ce ya dauki alhaki". Jam'iyyar Liberal Democrats  ta kayar da masu ra'ayin rikau na Conservative a Tiverton da Honiton, mazabar da ke kudu maso yammacin Ingila, yayin da jam'iyyar Labour, babbar jam'iyyar adawa, ta kwato mazabar Wakefield a arewacin Ingila.

Zabukan sun gudana ne bayan murabus biyu da tsaffin ‘yan majalisa masu ra'ayin rikau suka yi a watannin baya-bayan nan. Sannan ya zo makonni biyu bayan tsira da Firaministan Johnson ya yi daga kuri'ar yakar kauna da aka kada a majalisa. Sai dai a lokacin da ya je Ruwanda don halartar taron Commonwealth, Boris Johnson ya yi watsi da matakin yin murabus daga mukaminsa ko da ya sha kaye.

 


News Source:   DW (dw.com)