Birtaniya: Conservatives ta sha kaye

Birtaniya: Conservatives ta sha kaye
Jam'iyyar Conservatives ta su firaminista Boris Johnson a Birtaniya ta sha kaye a zaben cike gurbi da aka gudanar. Wannan wani mataki ne da ke zama koma baya ga jam'iyyar mai mulki.

Jam’iyyar masu ra’ayin 'yan mazan jiya ta Birtaniya wato Conseratives ta sha kaye a zabuka biyu da aka gudanar domin cike gurbin wasu 'yan majalisar dokokin kasar da suka yi murabus.

 A zaben cike da aka gudanar a ciki har da mazabar da ke kudu maso yammacin Ingila inda jam’iyyar ta kwashe sama da karni guda tana rike da yanki.

Jam'iyyar Liberal Democrats ta hambarar da masu rinjaye na Conservative don lashe gundumar Tiverton da Honiton, mazabar da ke kudu maso yammacin Ingila da ke da yawan 'yan ra'ayin mazan jiya da fiye da kuri'u 6,000.

A halin da ake ciki Shugaban jam'iyyar Conservative Oliver Dowden ya sanar da murabus dinsa ga firaminista Boris Johnson a yau Juma'a bayan mumunan sakamakon zaben da jam'iyyar ta su ta samu da ke zama babban koma baya a gare su.
 


News Source:   DW (dw.com)