Kasar Mali ta bayyana cewa sojoji masu binciken sun kaddamar da neman sanin hakikanin abin da ya faru a kauyen Moura a ke zargin aikata kisan kare dangi. Mai gabatar da kara na soja ya ce bayan zargin cin zarafin fararen hula da aka samu, hukumomi sun kaddamar da bincike.
A farko wannan wata na Afrilu sojojin Mali sun bayyana halaka tsageru 203 a garin na Moura, amma daga bisani rahotanni daga kafofin sada zumunta na zamani suka nunar da cewa kisan kare dangi sojojin suka aiwatar.
Hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta ce sojojin Mali da mayakan kasashen ketere sun halaka fararen hula kimanin 300 a Moura. Rasha take samar da abin da ta kira masu horas da sojoji ga kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka. Sai dai kasashen Amirka da Faransa gami da wasu kasashe sun ce masu ba da horon sojojin hayan ne na kamfani mai zaman kansa na Wagner na kasar ta Rasha.