Binciken cuta a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Hukumar kula da Lafiya ta Duniya ta tura kwararru zuwa kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, domin taimakon hukumomin kula da lafiya na kasar gano cutar da ta barke wadda ta halaka mutane da dama. Tawagar ta kunshi kwararrun likitoci daga bangarori da dama.

Karin Bayani: An kaddamar da aikin yaki da kyandar Biri a Kwango

Ofishin kular lafiyar ta duniya mai kula da nahiyar Afirka ya tabbatar da haka. A makon da ya gabata hukumomi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suka bayyana bullar cutar wadda ta kama kusan mutane 400 tare halaka mutane 30. Sai dai wasu rahotanni na cewa mutanen da wannan sabuwar cuta da ba a tantance ba ta halaka sun kai 130.

 


News Source:   DW (dw.com)