Hukumar ilimi da kimiya da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta saka hawan Daba na Kano a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya. Hawan Daban da ake gudanarwa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sau biyu a shekara a yayin bikin babba da karamar Sallah, ya samu shiga matakin ne bayan kwakwaran nazari kan abubuwan al'ada masu dumbin tarihi da ke tattare da shi.
Karin bayani : Musulmi na gudanar da babbar Sallah ta 2024
Mai magana da yawun hukumar ilimi da kimiya da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Hajo Sani, ta bayyana cewa bikin na samun dumbin mahalarta daga sassan kabilu daban daban, kama daga Hausawa da Fulani da Yarbawa da Bugaje da ke da zama a kasar Hausa.
Karin bayani : Bikin Sallar layya na Musulmai
A tsakiyar watan Yunin wannan shekarar ta 2024, hukumomin 'yan sanda a Kano sun dakatar da hawan Daban, bisa abubuwan da suka kira shawo kan matsalolin tsaro mai nasaba da darewar masarautar Kanon gida biyu.