Biden zai ba wa Kiev taimakon dala miliyan 800

Biden zai ba wa Kiev taimakon dala miliyan 800
Shugaba Joe Biden ya ce Amirka da kawayenta za su goyi bayan Ukraine don tabbatar da cewa kasar Rasha ba ta yi nasara a kanta ba.

Shugaban Amirka Joe Biden, ya ce gwamnatinsa za ta sanar da karin taimakon dala miliyan 800 na makamai ga Ukraine a cikin kwanaki masu zuwa. Wannan wani mataki ne da Washington ke dauka na nuna goyoyn bayan Kiev na kare kanta daga mamayar Rasha.

"Za mu goyi bayan Ukraine muddin bukatar hakan ta taso" inji Biden yayin taron manema labarai a gefen taron kungiyar tsaro ta NATO a birnin Madrid na kasar Spain. Ya kuma kara da cewa "Za mu tsaya tare da Ukraine, kuma dukkanin kawancen za su ci gaba da kasancewa tare da Ukraine, muddin dai ana bukatar ganin Rasha ba ta ci narasa ba." inji Biden.

Biden ya kara da cewa "Ukraine ta riga ta yiwa Rasha mummunan rauni," ya kara da cewa "bai san yadda za a kawo karshenta ba, amma hakan ba zai kare ba da kayen da Rasha ta yi wa Ukraine."


News Source:   DW (dw.com)