Biden ya yi afuwa ga masu laifi 1,500

Shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya ce zai yi afuwa ga mutane 39 wadanda aka yanke wa hukunci kan kananan laifuka yayin da kuma zai yi wa wasu mutanen 1,500 sassauci kan hukuncin da aka yanke musu na zaman gidan yari.

Afuwar na zuwa bayan fiye da mako guda da shugaban kasar ya sanya hannu kan wata doka inda ya yi wa dansa Hunter afuwa.

Jami'ai sun ce fadar White House ta saurari bukatun al'umma da suka nemi Biden ya yi afuwa kamar yadda ya yi wa dansa ga dubban jama'a da tsarin shari'ar Amurka ta yi musu adalci ba.

 


News Source:   DW (dw.com)